PDP na bukatar dan takara mai mutunci da martaba domin lashe zaben 2019 - Turaki

PDP na bukatar dan takara mai mutunci da martaba domin lashe zaben 2019 - Turaki

- Kabiru Turaki ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na bukatar daukar mutun mai martaba da mutunci a matsayin dan takarar shugaban kasa idan har tana so ta lashe zaben shugaban kasa a 2019

- Turaki dai ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa karkashin lemar PDP

- Ya ce zai mayar da hankali wajen kawo chanji ta fannin tsaro, sake fasalin lamuran kasar da kuma inganta tattalin arziki

- Dan takarar yace shi ne ya cancanci karawa da Shugaba Buhari a zabe mai zuwa

Daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Kabiru Turaki, ya bayyana cewa jam’iyyar na bukatar daukar mutun mai martaba da mutunci a matsayin dan takarar shugaban kasa idan har tana so ta lashe zaben shugaban kasa a 2019.

Tsohon ministan na ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin ya fadi hakan ne a Benin, jihar Edo yayinda yake jawabi ga tawaga da mambobin PDP kan kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Turaki yace shi ya cancanci kalubatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2019, inda ya kara da cewa kasar Najeriya na bukatar ba wai dan takara da ya san kan aiki ba kadai harda mai tarin ilimi kuma wanda baida bodadden hali.

Yace ya zama dole irin wannan dan takara ya kasance ba wadda aka sani da amfani damar tsarin lokacin da aka bashi damar shugabanci.

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai tsakanin wasu manya a APC da Gwamnonin Jihohi

Yace idan aka bashi tikiti kuma ya zama shugaban kasa, zai mayar da hanakali ne ga lamarin sake fasalin lamuran kasar da kuma tsaro domin tabbatar da ingantaccen tattalin arziki, inda ya kara da cewa matsalar Najeriya taki ci taki cinyewaa ne saboda ana take dokar kasar ta yadda ba’a tabbatar da adalci da daidaito.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babban jigon Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa kato-bayan-kato za a tsaya a fitar da ‘Yan takarar APC da su rike tuta a babban zabe mai zuwa.

Wasu dai a Jam'iyyar APC sam ba za su yarda da hakan ba. Irin wannan zabe ne dai aka yi kwanan nan wajen tsaida ‘Dan takarar Gwamnan APC a Jihar Osun. Ana tunani wannan tsari zai ragewa Gwamnoni karfi tare da kuma rage kashe kudi da ake yi wajen samun tikitin Jam’iyya inji wani Sanatan Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel