Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

- Bayan garkuwa da daliban makarantar Chibok a baya 'yan Boko Haram sun sake sace daliban makarantar Dapchi

- Ya zuwa yanzu dai sun sako ragowar daliban Dapchin amma sun rike guda daga cikinsu mai suna Leah Sharibu

- Muryarta ta bulla, yayinda take neman taimakon a ceto ta

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa tana sauraron sakamakon bincike daga rundunar tsaron farin kaya ta DSS akan batun muryar Leah Sharibu, dalibar makarantar Dapchi dake jihar Yobe, wacce ‘yan tayar da kayar baya na Boko Haram suka rike ta bayan sace ‘yan makarantar.

Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

Idan za'a iya tunawa dai a ranar 19 ga watan fabarairu ne mayakan kungiyar Boko Haram suka sace daliban makarantar Dapchi su kimanin 110. A inda suka rike Leah Sharibu bisa kin ta fita daga addinin da ta yi imani da shin a Kiristanci.

Sai ga shi a jiya Litinin muryar Leah Sharibu ta bulla, inda wasu kafafen yada labarai suka wallafa.

KU KARANTA: Na yi farin cikin jin muryan diyata – Mahaifin Leah Sharibu

“Ni ce Leah Sharibu dalibar nan ta makarantar Dapchi da mayakan Boko Haram suka sace. Ina kira ga shugaban kasa tare da sauran al'umma da su yi kokari su kubutar da ni daga halin da na ke ciki. Sannan ina rokon al'umma da su taimaki mahaifiyata da mahaifina tare karamin kanina.

Ku taimakamin ku kubutar da ni daga halin da nake ciki, ina rokonku da taimake ni, ina rokon gwamnati musamman shugaban kasa da ya ji tausayi na ya kubutar da ni daga halin da nake ciki".

Tun da farko dai babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai Mal. Garba Shehu ne ya bayyana matsayar fadar shugaban kasar a shafinsa na sada zumunta.

“Muna sane da muryar yarinyar nan da mayakan Boko Haram suka sace, kuma muna takaici tare da bakin cikin halin da take ciki".

“Jami'an tsaron rundunar farin kaya ta kasa suna bincike akan muryar, bisa hakan ya sanya muke sauraron sakamakon binciken na su, domin ganin an dawo da dalibar gida cikin ‘yan uwanta".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel