Birtaniya ta dawowa Najeriya da £70m, ta yi alkawarin dawo da kari

Birtaniya ta dawowa Najeriya da £70m, ta yi alkawarin dawo da kari

Gabanin zuwa Firam Ministan Birtaniya nan Najeriya, gwamnatin kasar ta dawowa Najeriya da wasu makudan kudi da wani ma’aikacin gwamnatin Najeriya ya kai kasar.

Kasar Birtaniya ta dawowa Najeriya da makudan kudi £70m da aka kwato daga hannun wani barawon gwamnati da ya sace kuma wata kotun Italiya ta kamashi.

Jakadan Birtaniya zuwa Najeriya, Mr Paul Arkwright, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Birtaniya ta dawowa Najeriya da £70m, ta yi alkawarin dawo da kari

Birtaniya ta dawowa Najeriya da £70m, ta yi alkawarin dawo da kari

Yace: “Akwai wata karar kotun Italiya da wani mutum. Wani kashin kudin na ajiye kasar Birtaniya kuma an maido da kudin Najeriya kwanan nan. Saboda hakane aka dawo da Fam milyan 70."

Amma jakadan Mr Paul Arkwright,ya ki bayyana sunan dan Najeriyan da aka ya kai kudin Najeriya waje.

Ya ce za’a dawo da karin kudi inda ya jaddada cewa kasarsa na aiki da gwamnatin Najeriya domin kara saurin gudun yadda za’a dawo da su.

“Gwamnatin kasar Birtaniya ba tada niyyar rike kwabo daya na kudin Najeriya a kasar Ingila, wajibi ne a dawo da su Najeriya.”

“Kamar yadda aka sani, kasar Birtaniya tanada ra’ayin cewa bin doka filla-filla na da muhimmaci kafin a dawo da kudaden.”

Arkwright ya tabbatar da cewa Firam Ministan Birtanya, Theresa May, za ta kawo ziyara Najeriya gobe Laraba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel