Gwamnatin tarayya: Babu wanda zai Musuluntar da Nigeria

Gwamnatin tarayya: Babu wanda zai Musuluntar da Nigeria

- Boss Mustapha ya tabbatarwa mabiya addinin Kirista cewa babu wanda zai iya Musuluntar da Nigeria

- Ya fadi hakan ne a wani taro mai taken, "Dorewar zaman lafiya da tsaro a arewacin Nigeria shine tushen ci gaba"

- Daga karshe sakataren gwamnatin ya roki mabiya addinin kirista da zasu zamo masu wanzar da zaman lafiya a kasar.

A ranar litinin ne gwannatin tarayya ta karyata zargin da ake yi na cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na son Musuluntar da kasar baki daya.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana wannan zargi a matsayin 'shaci-fadi' da makiyan kasar ke amfani da shi don haddasa rikicin addini.

Sakataren gwamnatin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wani taron wanzar da zaman lafiya na kwanaki biyu da kungiyar mabiya addinin kirista ta Nigeria CAN ta shirya.

Taron na da taken, "Dorewar zaman lafiya da tsaro a arewacin Nigeria shine tushen ci gaba"

Daga cikin mahalarta taron akwai ministan ma'aikatar aikin Noma, Chief Audu Ogbeh; Ministan wasanni, Solomon Dalung; da kuma mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Martins Babale.

KARANTA WANNAN: Kasar Amurka ta ce an samu karuwar cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari

A jawabin da Mustapha ya gabatar, ya ce dole ne Kiristoci suyi kunnen uwar shegu da wannan jita jitar, domin kuwa babu wanda zai iya kawo karshen addinin nasu.

A cewarsa, akwai bukatar kiristoci a Nigeria su rungumi koyarwar Isah Almasihu, wanda yayi nuni da soyayya ga juna, ba tare da nuna banbancin addini ba.

Ya ce: "Shin wane shiri ne mukayi a matsayinmu na kirista? Ya kamata ace muna da wani shiri wanda zai kawo zaman lafiya da soyayya a tsakaninmu dama mabiya addinin Musulunci; dole ne mu fita mu nuna kyawawan halayenmu, ba wai mu zauna waje daya a cikin duhu ba.

"A dai dai wannan gabar, ya zama wajibi in karyata wani zargi da ke yawo, na cewar shugaban kasa Buhari na son musuluntar da Nigeria; babu wanda wanda zai iya musuluntar da kasar nan. Ina son kowa a majami'ar nan ya san cewa babu mai iya kawo karshen addinin Kirista, don haka mu zamo masu wanzar da zaman lafiya a kasar," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel