Gwamnatin Buhari ba za ta iya shawo karshen matsalar talauci da tattalin arziki ba inji Atiku

Gwamnatin Buhari ba za ta iya shawo karshen matsalar talauci da tattalin arziki ba inji Atiku

NAIJ Hausa ta fahimci cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda yake neman mulkin Najeriya ya kuma yin kaca-kaca da Gwamnatin Muhammadu Buhari a shafin sa na sada zumunta na Tuwita.

Gwamnatin Buhari ba za ta iya shawo karshen matsalar talauci da tattalin arziki ba inji Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Atiku yace Buhari ya gaza

Alkaluma sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya bai bunkasa yadda ake tunani ba a watannin da su ka wuce. Wannan dalili ne ya sa Atiku Abubakar yace yake neman takarar shugabancin kasar nan a karkashin PDP a 2019.

Alhaji Atiku Abubakar yace rahotannin da aka saki kwanan nan sun nuna cewa babu wata nasarar da ake samu a bangaren tattalin arziki kuma ba a kai ga ci ba wajen ganin Najeriya ta rage dogaro da fetur kamar yadda ake fada.

KU KARANTA: Atiku yayi magana game da batun barin sa Jam’iyyar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar yace babu yadda Gwamnatin Buhari za ta iya magance matsalar tattalin arzikin da Najeriya ke ciki da kuma masifar talaucin da yayi wa daukacin mutanen Kasar katutu don haka a zabe sa.

Atiku Abubakar yace a lokacin da yake rike da mukamin Mataimakin Shugaban kasa, an ga bunkasa wajen harkar tattali. Ya kuma ce duk cikin masu neman takararar Shugabancin kasar nan babu wanda ya samawa mutane aikin yi irin sa.

Yanzu haka dai an ga abubuwan da ba a so bo a rahoton da Hukumar tara alkaluma na NBS ta saki game da tattalin arzikin kasar nan. Rashin habakar tattalin arikin ya kuma yi sanadiyyar raguwar kudin kasar wajen Najeriya inji masana tattali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel