Wani ‘Dan jarida yana neman Naira Miliyan 200 a wajen Gwamnatin Najeriya

Wani ‘Dan jarida yana neman Naira Miliyan 200 a wajen Gwamnatin Najeriya

Jones Abiri, wani ‘Dan Jarida ne da yake kukan an garkame sa babu gaira babu dalili don haka yake karar Gwamnatin Najeriya a Kotu inda yake neman a biya sa makudan kudi har Naira Miliyan 200.

Wani ‘Dan jarida yana neman Naira Miliyan 200 a wajen Gwamnatin Najeriya

An shigar da karar Gwamnatin Buhari a Kotun Tarayya a Abuja
Source: Facebook

Wannan Bawan Allah da aka saki kwanan nan ya shigar da karar Gwamnatin Tarayya a gaban babban Kotun Tarayya da ke Abuja bayan ta rufe sa na tsawon shekaru fiye da 2 ba tare da an mika shi Kotu domin ayi masa shari’a ba.

Yanzu haka dai har an fara zama a wani babban Kotun kasar da ke babban Birnin Tarayya Abuja inda mai karar yake tuhumar DSS da keta masa hakki da ci masa mutunci na tsawon watanni 24 sa'ilin da yake garkame a hannun DSS.

KU KARANTA: Na yi nadamar goyon bayan Shugaba Buhari a baya - Kwankwaso

Femi Falana wanda shi ne babban Lauyan da ke kare wannan ‘Dan Jarida watau Jones Abiri ya fadawa Kotu cewa garkame san da aka yi ba tare da an mika sa gaban Alkali ba ya sabawa dokar kasa da kuma hakkin ‘Dan Adam a Najeriya.

Lauyan da ke kare Hukumar DSS watau G,O Agbadua ya nemi Kotu ta basu dama su duba lamarin. Hakan ya sa dai Alkali mai shari’a bai zauna yayi hukunci game da karar da aka kawo masa ba a Ranar Litinin dinnan kamar yadda mu ka ji.

Gwamnatin Tarayya ta kama Jones Abiri mai shekaru 50 a Duniya tun Yulin 2016 ba tare da an shiga kotu da shi domin ayi shari’a ba. Sai kusan a watan jiya ne aka bada belin wannan Baawan Allah kuma hakan ya jawowa Gwamnati suka sosai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel