Kungiyar Afenifere ta nemi Buhari ya hakura da mulki bayan Trump ya caccake sa

Kungiyar Afenifere ta nemi Buhari ya hakura da mulki bayan Trump ya caccake sa

Labari ya zo mana cewa Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi magana bayan an ji cewa Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya caccaki Takwaran sa Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kwanaki.

Kungiyar Afenifere ta nemi Buhari ya hakura da mulki bayan Trump ya caccake sa

An fara hurowa Buhari ya sauka daga mulki bayan 2019

An nemi Shugaban kasa Buhari ya hakura da mulki bayan 2019 saboda abin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya fada game da Shugaban. Kungiyar Afenifere tace tabbas akwai bukatar a samu Shugaba mai cike da koshin lafiya.

Kungiyar da ke magana da yawun Yarbawa tace ya kamata a samu Shugaban kasa mai lafiya da katabus domin cigaba da jan ragamar kasar na shekaru 4 masu zuwa nan gaba inji Sakataren yada labarai na wannan Kungiyar na kasa.

KU KARANTA: Jawabin PDP bayan Trump ya soki Shugaban Najeriya

Yinka Odumakin wanda shi ne Sakataren yada labaran Afenifere ya bayyanawa Jaridar Premium Times cewa ko da an san Donald Trump da tafka katabora, sai dai abin da Shugaban na Amurka ya fada game da Shugaba Buhari gaskiya ne.

Afenifere tace mulkin Najeriya yana cikin aikin da ya fi kowane wahala a Duniya don haka ake bukatar mai jini a jika ba wanda aka sani da fama da rashin lafiya ba. Odumakin ya nemi Buhari ya bar mulki idan ya cika wa’adin sa a 2019.

Mun samu labari cewa yanzu haka wata Kungiya da ke goyon bayan Shugaban kasa Buhari dai tayi tir da abin da ake kishin-kishin din Donald Trump ya fada game da Shugaba Buhari bayan wata haduwa da su kayi a Amurka kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel