Buhari ba zai huta ba har sai an dawo da Leah Sharibu da sauransu gida – Fadar shugaban kasa

Buhari ba zai huta ba har sai an dawo da Leah Sharibu da sauransu gida – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa tayi martani akan maganar da Yar makaratan Dapchi tayi

- Ta bukaci gwamnati ta ceci rayuwarta

- Fadar shugaban kasar tace Buhari ba zai huta ba har sai ya ceto Leah da sauran mutane

Fadar shugaban kasa tayi martani akan wani faifan Magana dake yawo na muryar aka ce mallakar Leah Sharibu ne inda ta bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo mata tallafi.

A wata sanarwa daga Garba Shehu wanda ya kasance babban mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, yace shugaban kasar na sane da faifan muryan sannan kuma cewa jami’an sirri na aiki akai.

Buhari ba zai huta ba har sai an dawo da Leah Sharibu da sauransu gida – Fadar shugaban kasa

Buhari ba zai huta ba har sai an dawo da Leah Sharibu da sauransu gida – Fadar shugaban kasa

Shehu yace gwamnatin ta mayar da hankali waje dawo da Leah da sauran mutan da yan Boko Haram suka sace gida.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Leah Sharibu, Daya daga cikin yan matan Dapchi 119 da yan tada kayar bayan Boko Haram suka sace a makarantan sakandaren gwamnati na mata a garin Dapchi, jihar Yobe, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ceceta.

Leah Sharibu ce kadai ba’a saki ba lokacin da aka saki sauran yan matan saboda ta ki sauya addininta zuwa Musulunci.

A wani hoto da odiyo na nuna cewa tana da rai. Jaridar The Cable ta samu rahoto na musamman da ya kunshi hotonta da gajeren jawabi.

A jawabin, ta bukaci Buhari ya cetota kuma a taimakawa iyayenta da sauran iyalai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel