Wuta ta cinye kananan yara 2 yan gida daya a wata mummunar gobara a Delta

Wuta ta cinye kananan yara 2 yan gida daya a wata mummunar gobara a Delta

Rai bakon duniya inji masu iya magana, haka zalika kowa ka gani lokacinsa kawai yake jira, kamar yadda wasu kananan yara suka gamu da ajalinsu a sakamakon wata mummunar gobara data tashi a gidansu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gobarar ta samu asali ne daga wani kyandir da kakar yaran ta kunna a dakinsu don samun haske sakamakon yan NEPA basu kawo wuta ba, daga nan ne wutar kyandirin ya kama wani jarkar gurbataccen kalanzir da kakar ta sayo, hakan ne ya haifar da tashin wuta a gidan.

KU KARANTA: Mummunar dabi’a: Yansanda sun kama yan luwadi guda 57 a jihar Legas

Rahortanni sun bayyana sunayen kananan yara kamar haka; Wealth Enorke dan shekara 1, da Kesiena Lucky mai shekaru hudu a rayuwa, dukkaninsu yayan wasu mata biyu yan uwan juna, Elorho Lucky da Ufuoma.

Gobarar da ya tashi a gidan kakar dake yankin Igbudu cikin karamar hukumar Warri ta kudu na jihar Delta ya rutsa da kimanin yara shida zuwa bakwai, sai dai tsohuwar ta yi ta maza, inda ta dinga kutsa kai cikin wutar har sai da ta ceto yara hudu daga cikinsu.

Sai dai duk kokarin da tayi, sai da wutar ta cinye jikokinnata guda biyu, kamar yadda guda daga cikin uwayen yaran ta shaida cewa “Na fita daga dakin Mama Sola, na tafi dakin Tuwere, ina can ne aka fada min gobara ya tashi a dakinmu da misalin karfe biyu na dare.”

A nasa jawabin, Kwamishinan Yansandan jihar, Mohammed Mustafa ya tabbatar da faruwar gobarar, wanda ta lashe rayukan yara biyu da dukiyoyi na miliyoyin nairori.

Ku biyo mu a Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel