Ebola ta salwantar da rayuwar mutane 67 a jihar Congo

Ebola ta salwantar da rayuwar mutane 67 a jihar Congo

Akalla mutane sittin da bakwai ne suka gamu da ajalinsu sakamakon sake barkewar cutar Ebola a kasar jamhuriyar dimukradiyyar Congo, inji rahoton jaridar TheCable.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jami’in ma’aikatar lafiya, ALred Longi ya bayyana cewa sun samu rahoton kamuwar mutane 105 da wannan muguwar cuta a jihar Congo, musamman a lardin Ituri da Arewacin Kivu.

KU KARANTA: Mummunar dabi’a: Yansanda sun kama yan luwadi guda 57 a jihar Legas

Alfred yace an tabbatar da kamuwar cutar akan mutane 77 daga cikinsu, mutane 11 sun warke, 27 kuma an kwantarsu, yayin da 67 suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar kamuwa da cutar Ebola.

Ebola ta salwantar da rayuwar mutane 67 a jihar Congo

Ebola

Alfred ya cigaba da fadin a yan kwanakin nan ya je cibiyar kula da masu cutar Ebola dake Mangina, inda a gabansa aka sauke wasu mutane biyu da suka warke daga cutar.

“Mutane biyu da aka sallamosu na daga cikin mutane biyar da aka yi musu gwajin cutar a jikinsu, inda sakamakon gwajin ya nuna sun warke, babu sauran kwayar cutar a tare dasu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, a ranar Juma’ar data gabata ne cibiyar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, ta taya kasar Congo murnar fara shawo kan cutar Ebola da ta watsu a wasu sassan kasar, wannan shine karo na 10 da cutar Ebola ta barke a kasar Congo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel