PDP ta mayar da martani akan furucin Trump game da Buhari

PDP ta mayar da martani akan furucin Trump game da Buhari

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta tace Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na kewaye dashi sun bude kafar da kasashen waje zasu mayar da kasar abun dariya daga rahoton da aka ce shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana Buhari a matsayin “gawa”.

Jam’iyyar PDP a wata sanarwa da sa hannun Kola Ologbondiyan, babban sakataren labaranta na kasa, yace irin wannan tozarcin na samun kasa ne idan bata da gawurtattun shugabanni, masu yawo a fadin duniya, don kawai suna Allah Allah su ga sun samu karbuwa daga shugabannin duniya.

PDP ta mayar da martani akan furucin Trump game da Buhari

PDP ta mayar da martani akan furucin Trump game da Buhari

Jam’iyyar tace Shugaba Buhari ya dade yana neman suna a idanun duniya wadda babu alamun wasu nasarori daga shearu ukun da yayi akan mulki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da martani ga shugaban kasar Amurka, Donald Tump kan ikirarin da aka ce shugaban Amurkan a bayyana shugaban Najeriya a matsayin “gawa” , jaridar Vanguard ta ruwaito.

Martanin wadda ya fito ta hannun kungiyar abaran Buhari (BMO) martani ne ga rahoton da jaridar Financial Times ta wallafa aranar Litinin, 7 ga watan Agusta cewa Shugaban kasar Amurka yayi mumunan kalami akan lafiyar Shugaba Buhari.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

“Shugaba Muhammadu Buhari na da koshin lafiya kuma zai iya tsayawa takarar zabe a 2019 kuma ya gudanar da lamuran kasar tsawon shekaru hudu, maganar Donald Trump bai da tushe”, inji kungiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel