Babu wani jami’in Rivers da zai gurfana a gaban EFCC – Wike ga Magu

Babu wani jami’in Rivers da zai gurfana a gaban EFCC – Wike ga Magu

- Gwamnan jihar Rivers yayi raddi ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa

- Yace babu wani jami’i daga gwamnatin jihar da zai gurfana a gaban hukumar tra EFCC

- Hakan ya biyo bayan gayyatar Peter Amangho, manajan darakta na bankin Zenith da hukumar tayi tare da yi masa tambayoyi akan zargin naira biliyan 117 da gwamnatin jihar ta fitar

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike yace babu wani jami’i daga gwamnatin jihar da zai gurfana a gaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattaln arziki zagon kasa (EFCC).

Wike yayi magana ne bayan hukumar EFCC ta gayyaci Peter Amangho, manajan darakta na bankin Zenith tare da yi masa tambayoyi akan zargin naira biliyan 117 da gwamnatin jihar ta fitar cikin shekaru uku da suka gabata.

Babu wani jami’in Rivers da zai gurfana a gaban EFCC – Wike ga Magu

Babu wani jami’in Rivers da zai gurfana a gaban EFCC – Wike ga Magu

Wike ya zargi hukumar da sanya siyasa a bincike, inda ya kara da cewa har sai idan hukumar ta tunkari kotun daukaka kara domin ajiye hukuncin 2007 wadda ya hana hukumar yin binciken jihar, jami’anta ba zasu amsa gayyatar ta ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

A cewar jaridar TheCable, wani jami’in EFCC ya bayyana yadda aka cire kudaden.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel