2019: PDP tayi alkawarin yin zaben gaskiya-da-gaskiya wajen tsaida ‘Yan takara

2019: PDP tayi alkawarin yin zaben gaskiya-da-gaskiya wajen tsaida ‘Yan takara

Mun samu labari cewa yanzu haka PDP ta fara shirin yadda za ta dumfari zaben 2019 da kyau domin ta iya tika Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan da kasa. Nan da watanni 6 ne za ayi babban zabe a kasar.

2019: PDP tayi alkawarin yin zaben gaskiya-da-gaskiya wajen tsaida ‘Yan takara

Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Prince Uche Secodus

Shugaban Jam’iyyar adawar ta PDP na Jihar Delta Kingsley Esiso ya bayyana cewa dole PDP ta hada kan ‘Ya ‘yan ta kafin a shiga zaben na 2019. Esiso yace ba zai yiwu Jam’iyyar ta yi nasara a zaben 2019 ba idan babu hadin-kai.

Jam’iyyar tayi alkawarin shirya zabe mai inganci cike da nagarta domin tantance wadanda za su rike mata tuta a 2019. PDP tace ba za ta sake 2019 ta zo ba tare da an samu hadin-kai da fahimtar juna a cikin manyan ‘Yan Jam’iyyar ba.

KU KARANTA: Shugaban PDP ya sauya sheka zuwa APC a Legas

Shugaban PDP na Jihar Delta ne dai ya sanar da wannan a bakacin Jam’iyyar adawar. Kingsley Esiso ya nuna cewa PDP za ta bar kowa ya taka rawar ganin sa watau wanda ya iya allon sa ya wanke a zaben fitar da gwani da za ayi a kwanannan.

Shugaban PDP na kasa Prince Uche Secondus dai yace Matasa za a bari su ja ragamar Jam’iyyar bayan zaben 2019. Hakan na zuwa ne bayan Ahmad Makarfi ya bayyana dalilan da su ka sa ya fi su Atiku dacewa da tikitin PDP a zaben mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel