Tsagerun yankin Neja-Delta sun yi barazanar komawa kai hare-hare

Tsagerun yankin Neja-Delta sun yi barazanar komawa kai hare-hare

Tsagerun yankin Neja-Delta, karkashin hadakar kungiyoyin dake fafutikar neman 'yancin yankin, sun yi barazanar komawa kai hare-hare matukar gwamnatin tarayya ta ki amincewa da yiwa kundin tsarin mulkin kasa garambawul.

A wani jawabin da shugaban hadaddiyar kungiyar, Mista John Duku, ya saka wa hannu kuma aka raba ga manema labarai ranar Asabar a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom, tsagerun sun ce yin barazanar ya zama dole ganin yadda gwamnatin jam'iyyar APC ke gudanar da salon mulkinta.

Tsagerun yankin Neja-Delta sun yi barazanar komawa kai hare-hare

Tsagerun yankin Neja-Delta

A cewar Duku, "bayan mun yi nazarin yadda abubuwa ke gudana a karkashin gwanatin tarayya musamman a kan al'amuran da suka shafi yankin Neja-Delta, muna son mu zayyana wasu bukatun mu kamar haka:

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun yiwa mayakan kungiyar Boko Haram rugu-rugu a jihar Borno

"Muna masu nuna takaicin mu da yin amfani da hukumar EFCC wajen rufe asusun ajiyar jihar Akwa Ibom. Muna son sanin dalilin da ya sa hukumar EFCC ke muzgunawa jihohin jam'iyyar adawa da kuma dalilin da yasa basa ganin laifin cin hanci a jihohin da jam'iyyar APC ke mulki?, a cewar Duku.

kazalika jawabin Dukku ya yi tsokaci a kan al'amuran makiyaya da kuma yadda ake tsangwamar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki tare da yin barazanar cigaba da kai hare-hare matukar ba a daina matsa wa wadanda ke adawa da jam'iyyar APC ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel