Da duminsa: Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC

Da duminsa: Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC

Cif Moshood Salvador, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas da aka cire daga mukaminsa ya bayyana canja sheka zuwa APC a yau, Litinin.

Salvador ya dade yana fama da matsaninciyar adawa daga tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma dan asalin jihar Legas, Cif Bode George.

Salvador ya bayyana ficewar sa daga daga PDP a gidansa dake benen Salvador a cikin garin Legas.

Ko a jiya Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wasu masu taimakawa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, sun ja zugar mutane fiye da 5,000 zuwa jam'iyyar APC.

Da duminsa: Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC

Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC
Source: Depositphotos

Masu taimaka gwamnan su biyu sun bayyana ficewar su daga jam'iyyar PDP ne ranar Asabar yayin kaddamar da takarar tsohon hukumar tattarar haraji a jihar Delta, Onowakpo Thomas, dake neman jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isoko.

DUBA WANNAN: Ko a tsayar da ni takarar gwamna, ko a fadi zabe - Ministan Buhari ya yiwa APC barazana

Yayin kaddamar da takarar ne mataimakan gwamnan biyu; Lucky Arumare da Uyoyou Edhekpo, suka bayyana fitar su daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayansu fiye da 5,000

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel