Yaki da rashawa: Hukumar EFCC ta kama shugaban wani babban banki a Najeriya

Yaki da rashawa: Hukumar EFCC ta kama shugaban wani babban banki a Najeriya

Ba sani ba sabo, kuma babu shafaffu da mai, wannan shine kwatankwacin sakon da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ke aikawa a duk lokacin da aikinta ya taso a ciki da wajen kasar nan.

Hukumar EFCC ta yi ram da shugaban bankin Zenith, Mista Amangbo biyi bayan cire makudan kudi da gwamnatin jihar Ribas ta yi da suka kai naira biliyan dari da goma sha bakwai (N117bn), inji rahoton jaridar Premium Times.

KU KARANTA: Ya yi marisa ya sha kwaya: Yadda wani matashi ya halaka kansa bayan ya daddaki tabar wiwi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 23 ga watan Agusta ne hukumar ta fara gayyatar Amangbo, amma ta bada belinsa bayan ya sha tambayoyi, inda ta nemi ya koma a ranar 24, sai dai daga ranar 24 ne fa ta rike shi har yanzu babu labarinsa.

Yaki da rashawa: Hukmar EFCC ta kama shugaban wani babban banki a Najeriya

Amangbo

EFCC na zargin Amangbo da hadin baki wajen cire makudan kudaden da gwamnatin jihar Ribas ba tare da ya shaida ma hukumar ba, kamar yadda dokokin aikin banki ta tanadar, wanda ya iyakance adadin kudin da mutum ko kungiya zai iya cirewa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa EFCC na farautar wasu mutane hudu dake da hannu cikin wannan bahallatsa daga cikinsu akwai Fubara Similari wanda shine Daraktan kudi na fadar gwamnatin jihar Ribas, sai kuma jami’I mai bada kudi.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin masu magana da yawun bankin Zenith yaci tura, sakamakon kin amsa wayoyinsu, ko kuma amsa sakonnin karta kwana da yan jaridu suka aika musu.

A wani labarin kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya caccaki wannan bincike da EFCC ke yi, inda ya bayyana nata a matsayin bita da kulli, sa’annan yace ba zai bari wani jami’in gwamnatinsa ya gurfana gaban EFCC ba

Gwamnan yayi nuni da wata hukunci da kotun daukaka kara ta yi a shekarar 2007, wanda ta hana EFCC bin diddigin asusun gwamnatin jihar Ribas, bugu da kari yayi alkawarin shigar da EFCC kara gaban Kotu don a hanata shiga cikin harkokin jihar Ribas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel