An yi wa mata 79, maza 16 fyade cikin watanni 7 a Kaduna

An yi wa mata 79, maza 16 fyade cikin watanni 7 a Kaduna

- Kungiyar SARC da ke jihar Kaduna tayi tsokaci akan yawaitan lalata yara da ake yi

- Tace an shigar da kararraki da ya shafi yiwa mata fyade har 95 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli 2018

- Hadda maza a wadanda aka lalata

- Kungiyar ta ja hankalin iyaye a su zuba idanu sosai akan yaransu

Kungiyar kula da wadanda aka yi wa fyade (SARC) da ke jihar Kaduna ta bayyana cewa an shigar da kararraki da ya shafi yiwa mata fyade har 95 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli 2018.

Wata jigo kungiyar Juliana Joseph ta sanar da hakan a hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta a Abuja .

Ta kara da cewa bisa ga kararrakin da suka saurara a tsakanin wannan lokaci 16 daga cikin wadanda aka lalata maza ne.

An yi wa mata 79, maza 16 fyade cikin watanni 7 a Kaduna

An yi wa mata 79, maza 16 fyade cikin watanni 7 a Kaduna

Misis Joseph ta ce bisa ga bayanan da suka samu daga wajen wadanda aka yi wa fyaden sun nuna cewa 19 daga cikinsu makwabta ne suka aikata masu hakan, bakwai kuma masu gadin gidajen su, 10 kuma daga ‘yan uwa ne suka lalata su.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa fadar shugaban kasa ba zata yi raddi ga kalaman Trump a kan Buhari ba

“Wuraren da aka fi aikata wannan ta’asa a Kaduna sun hada da Tudun Wada, Kakuri Kudenden, Nasarawa, Hayin Banki, Gonin Gora, Dan Bushia, Romi da Rigasa.”

A karshe ta yi kira ga iyaye da su sa rika sanya idau kan ‘ya’yan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel