Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da Naira biliyan 2 don gina Jami'ar Sojoji

Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da Naira biliyan 2 don gina Jami'ar Sojoji

- A yunkurin gwamnatin kasar nan na magance matsalar, ta amince da kafa sabuwar jami'ar tsaro

- Jami'ar za ta zama irinta ta farko a kasar nan bayan ta horon Sojoji tun daga tushe ta NDA dake Kaduna

Gwamnatin tarayya ta amince da gina jami'ar Sojoji akan kudi kimanin Naira biliyan biyu, a garin Biu dake jihar Borno.

Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da Naira biliyan 2 don gina Jami'ar Sojoji

Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da Naira biliyan 2 don gina Jami'ar Sojoji

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin babban Sakataren kula da asusun tallafawa ilimi Dakta Abdullahi Baffa Bichi, a lokacin da shugaban rundunar Sojin kasar nan Laftanal Janar Tukur Buratai ya kai masa ziyara a ofishinsa dake Abuja.

KU KARANTA: Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin zabe da INEC ta nema

Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana cewa “Majalisar zartarwa ta amince da kudi kimanin Naira biliyan biyu domin gina jami'ar Sojoji a garin Biu dake jihar Borno. Zan kuma yi amfani da wannan dama wajen taya shugaban rundunar Sojin kasar nan tare da jami'ansa, bisa irin gagarumar nasarar da suka samu akan masu tayar da kayar baya, magance rikicin manoma da makiyaya da kuma fatattakar barayin Shanu a fadin kasar nan".

“Bisa irin wannan gagarumar nasarar da Sojin kasar nan suka samu, wanda hakan ya dunkule kasar nan waje guda. Muna fatan zamu cigaba da ganin nasarorin da za su cigaba da samu".

A nasa bangaren Janar Buratai ya ce jami'ar za'a yi ta ne bisa bukatun Sojin kasar nan, tare kuma da bunkasa harkokin kimiyya da fasaha a fadin kasar nan baki daya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel