Ya yi marisa ya sha kwaya: Yadda wani matashi ya halaka kansa bayan ya daddaki tabar wiwi

Ya yi marisa ya sha kwaya: Yadda wani matashi ya halaka kansa bayan ya daddaki tabar wiwi

Duniya kenan, yayin wasu ke shigowa cikinta, wasu kuma ficewa suke daga cikinta da gudu, sai dai abinda kowa ya kamata ya damu da shi shine hanyar mutuwar, walau kyakkyawar cikawa ko mummuna.

Anan rundunar Yansandan jihar Enugu ce ta sanar da mutuwar wani matashi mai shekaru 24 ta hanyar kashe kansa da kansa bayan daddaki tabar wiwi, sa’annan ta sanar da kaddamar da bincike game da lamarin, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ambaci mutane 4 da ba zai taɓa ɗaga musu ƙafa ba har abada

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Ebere Amaraizu ce ta tabbatar da mutuwar matashin a ranar Asabar, 25 ga watan Agusta a garin Enugu, inda tace lamarin ya faru ne a ranar Larabar data gabata.

Ebere ta bayyana sunan matashin a matsayin Ebube Chukwu, kuma mazauni ne a kauyen Ameke dake cikin karamar hukumar Aninri na jihar Enugu, inda tace ya kashe kansa ne bayan ya sha tabar wiwi da dama.

“Matashin ya kashe kansa ne ta hanyar rataye wuyarsa akan wani bishiya dake dajin Obokolo, sai dai jama’an kauyen sun shedi matashin da yawan shan tabar wiwi, inda suke ganin kamar illar wiwin ta kai shi ga halaka.” Inji ta.

Daga karshe Kaakaki Ebere Amaraizu tace a yanzu haka hukumar Yansandan jihar Enugu ta kaddamar da binciken kwakwaf akan lamarin don tabbatar da musabbabin mutuwar Ebubu Chukwu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel