Dalilin da yasa fadar shugaban kasa ba zata yi raddi ga kalaman Trump a kan Buhari ba

Dalilin da yasa fadar shugaban kasa ba zata yi raddi ga kalaman Trump a kan Buhari ba

Wata jaridar yankin Birtaniyya, Financial Times, ta rawaito cewar shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kira shugaba Buhari da "lusari" tare da bayyana cewar baya fatan su kara haduwa har abada.

Shugaba Buhari ya ce ba zai ce komai a kan kalaman na Trump ba saboda ba daga bakinsa aka ji maganar ta fito ba.

Mai taimakawa shugaba Buhari a kan yada labarai, Mista Femi Adesina, ya ce fadar shugaban kasa ba zata ce komai a kan abinda jaridar da rawaito ba saboda rashin tushe balle makama, kamar yadda ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC.

"Ku 'yan jarida ne, kun san duk zancen da aka ce an ji daga majiya maras tushe kun san ba gaskiya bane. Don ba zamu ce uffan ba a kan wannan batu ba," a kalaman Mista Adesina.

Dalilin da yasa fadar shugaban kasa ba zata yi raddi ga kalaman Trump a kan Buhari ba

Trump d Buhari

BBC ta ce Mista Adesina bai tsaya an karasa tambayoyin da wakilinsu ke yi masa ba ya katse kiran.

Kalaman na Trump sun jawo barkewar cece-kuce a dandalin sada zumunta tare da wasu 'yan Najeriya na jefa magana ga shugaba Buhari bisa kalaman da shugaba Rum ya yi.

DUBA WANNAN: 2019: Ko a bani takarar gwamna, ko APC ta fadi zabe - Ministan Buhari ya yiwa APC barazana

Wasu masu nazarin harkokin diflomasiyya na ganin cewar gwamnatin Najeriya ba zata yi raddi ga Trump bane saboda gudun lalacewar dangantaka mai kyau da gwamnatin Amurka da ta Najeriya ke da ita tun bayan hawan shugaba Buhari karagar mulki a 2015.

Kazalika sun kara da cewar shugaba Buhari ba zai so yin raddi a kan kalaman Trump a yanzu ba saboda hakan kan iya haifar da cece-kuce da zasu iya dauke hankalinsa wajen mayar da hankali kan lashe zaben shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel