Dalilin da ya sa ba zamu bar Buhari yayi takar shi kadai ba tare da zaben cikin gida ba - APC

Dalilin da ya sa ba zamu bar Buhari yayi takar shi kadai ba tare da zaben cikin gida ba - APC

- Da yiwuwar a samu wanda zai kayar da shugaba Buhari a zaben cikin gida na jam'iyyar APC

- APC ta jaddada aniyarta na baiwa kowa dama matukar yana da burin karawa da shugaban kasar

Duba da yadda zaben 2019 ke karatowa, jam'iyyar APC ta bayyana cewa shugaba Buhari ba zai samu tikitin takarar kasar nan ba karkashin jam’'iyyar ba saboda akwai wasu 'ya'yan jam'iyyar da suke muradin samun tikitin.

Dalilin da ya sa ba zamu bar Buhari yayi takar shi kadai ba tare da zaben cikin gida ba - APC

Dalilin da ya sa ba zamu bar Buhari yayi takar shi kadai ba tare da zaben cikin gida ba - APC

Mai yada labaran jam'iyyar APC na kasa Yekini Nabena, ya bayyana cewa jam'iyyar zata bawa kowa dama a zaben fidda gwanin da za’a yi duk da cewa shugaba Buhari yana da dama fiye da kowa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

Nabena ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da jaridar Daily Independent, inda ya shaida cewa "Za a yi zaben fidda-gwani domin a bawa kowa hakkinsa. Don haka maganar cewa shugaba Buhari zai samu tikiti ba tare da an yi zaben fidda-gwani ba, babu ita".

Da aka tuntube sa ko mutane nawa suke son yin takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar APC, Nabena ya shaida cewa ya zuwa yanzu dai bai wuce mutane biyu ba, amma da zarar an fara sayar da tikitin takarar za’a gane adadin mutanen dake son yin takarar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel