Shugaba Buhari ya ambaci mutane 4 da ba zai taɓa ɗaga musu ƙafa ba har abada

Shugaba Buhari ya ambaci mutane 4 da ba zai taɓa ɗaga musu ƙafa ba har abada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu jerin mutane guda uku da yayi alkawarin gwamnatinsa zata ga bayansu sakamakon ayyukan mugunta da suke aikatawa a tsakanin al’umma, musamman ta hanyar gurfanar dasu gaban shari’a.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Agusta, a shafinsa na Tuwita, inda yace a shirye yake ya kawo karshen duk wani barazanar tsaro da ya addabi kasarnan.

KU KARANTA: Leah Sharibu ta yi magana karo na farko a hannun Boko Haram

“Zan cigaba da neman dukkanin jami’an hukumomin tsaron Najeriya sun kawo karshen miyagun mutane masu satar shanu, yan bindiga da masu garkuwa da mutane, da duk wani mutumin dake ganin shi ya fi karfin doka a kasarnan, saboda sai tsaro ya tabbata a kasa ne za’a samu dawwamammen cigaba.” Inji Buhari.

Idan za’a tuna shugaba Buhari ya gana da Sojojin dake yaki da yan bindiga a jihar Zamfara, inda ya umarcesu da kada suyi sakwa sakwa da duk wani dan bindiga da suka yi arangama da shi, sa’annan ya bayyana jin dadinsa da cigaba da ake samu a sanadiyar ayyukansu.

“Na yaba da kokarin da jami’an runduar Sojan sama ke yi ta wajen yin ruwan wuta a duk inda yan bindigan suke, don kuwa zuwa yanzu yan Najeriya sun fara ganin amfanin aikin naku.” Inji shugaba Buhari.

Daga karshe Buhari ya yi alkawarin cigaba baiwa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke bukata don gudanar da aikinsu kamar yadda ya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel