Sanata daya tilo da PDP ke da shi a Rivers ya sauya sheka inda ya koma APC

Sanata daya tilo da PDP ke da shi a Rivers ya sauya sheka inda ya koma APC

- Wani Sanatan jihar Rivers ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

- Osinakachukwu ThankGod Ideozu ya kasance satana daya tak da PDP ke da shi a jihar

- Yan siyasa na ci gaba da sauye sauyen jam'iyya tun bayan da guguwar zaben 2019 ta kado

Sanata mai wakiltan mazabar Rivers ta yamma a majalisar dokokin kasar, Sanata Osinakachukwu ThankGod Ideozu ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’yyar All Progressives Congress (APC).

Har zuwa ranar da koma APC, Ideozu ya kasance sanatan PDP guda daga jihar Rivers a majaliar dokokin kasar yayinda Magnus Ngei Abe da Andrew Igbonule Uchendu, dake wakiltan jihar suka kasance yan APC.

Sanata daya tilo da PDP ke da shi a Rivers ya sauya sheka inda ya koma APC

Sanata daya tilo da PDP ke da shi a Rivers ya sauya sheka inda ya koma APC
Source: Depositphotos

Wata majiya ta bayyana cea za’a sanar da cikakken bayanin sauya shekar sanatan a gangami da za’a gabatar a mazabarsa, wanda shugaban jam’iyuyar na jihar bai sana rana a tukuna.

A kwanakin baya ne yan majalisar dokokin kasar da dama suka sauya sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa babban jam'iyyar adawar kasar.

A wani lamari na daban, Jam’iyyar APC mai mulki ta kalubalanci Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bude Majalisa idan har ba ya gudun Sanatoci su tsige sa daga kujerar sa kamar yadda yake fada.

Ta maidawa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki amsa bayan yace sam bai gudun a cire sa daga kujerar sa.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan siyasar da za su yi takarar Gwamna a Jihar Kwara a zaben 2019

Yekini Nabena wanda shi ne Sakataren yada labarai na APC na rikon kwarya ya fadawa ‘Yan jarida idan har Bukola Saraki yana ji ya isa, ya bude Majalisar ya gani ko za a iya tsige sa tare da bin dokar kasar nan ko kuma ba za a iya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel