APC zata fadi zabe muddin ba ta tsayar da ni takarar gwamna ba - Ministan Buhari

APC zata fadi zabe muddin ba ta tsayar da ni takarar gwamna ba - Ministan Buhari

Ministan sadarwa, Adebayo Shitu, ya yi ikirarin cewar APC zata fadi zaben gwamna a jihar Oyo muddin ba shine jam'iyyar ta tsayar takarar gwamna ba a zaben shekarar 2019.

Da yake ganawa da manema labarai a karshen sati, Shitu ya yi kurarin cewar shine kadai dan takarar APC da zai iya cin zaben gwamna a jihar cikin sauki tare da bayyana cewar da zarar ya samu tikitin takara a APC dukkan wadanda suka fita jam'iyyar a jihar zasu dawo.

"Ina mai tabbatar maku kamar yadda na tabbatar wa da shugabannin APC a jihar Oyo cewar nine kadai zabin da jam'iyyar da ke da shi: ko su bani takara ko kuma su sha kaye a hannun jam'iyyar adawa. Zan ci zabe cikin sauki idan aka bani takara saboda ina da goyon bayan mutanen jihar Oyo. Bana son nayi furuci marar dadi a kan jam'iyya ta amma matukar basu bani takara ba to su manta da batun cin zaben gwamna a jihar Oyo," a kalaman Shitu.

APC zata fadi zabe muddin ba ta tsayar da ni takarar gwamna ba - Ministan Buhari

Adebayo Shittu, Ministan Buhari

Shitu ya cigaba da cewa, "ko a zaben shekarar 2015 mutanen garin Ibadan basu zabi gwamna Ajimobi ba, sun gwammaci su zabi tsohon gwamna Rashidi Ladoja da ya tsaya a PDP. Mutane na na yankin Oke Ogun ne suka zubawa Ajimobi kuri'ar da ta bashi nasarar lashe zabe.

DUBA WANNAN: Dakarun sojin Najeriya sun yiwa mayakan kungiyar Boko Haram rugu-rugu a jihar Borno

"Saboda jin dadin goyon bayan da muka bashi, gwamna Ajimobi ya daukar wa mutane na alkawarin cewar dan takarar gwamna a zaben 2019 zai fito daga yankin ne sai dai abun takaici yanzu nema yake ya saba wannan alkawari da ya dauka."

Shitu ya bayar da tabbacin cewar ba zai fita daga APC ba amma zai cigaba da yakar duk wani rashin adalci a cikin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel