Siyen kuri'u: INEC zata sake fasalin rumfunar zabe kafin 2019

Siyen kuri'u: INEC zata sake fasalin rumfunar zabe kafin 2019

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce zata sake fasalin rumfunan zabe

- Hukumar ta roki kafafen watsa labarai dasu mara masu baya wajen tona asarin masu siyen kuri'u a wajen zabe

- Haka zalika, hukumar ta INEC ta ce ba zata samar da karin rumfunan zabe ba, sai bayan an kammala zaben 2019

Mr. Mustapha Lecky, kwamishinan hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa INCE na yankin Kudu maso Kudu, ya ce hukumar zata sake fasalin rumfunan zabe a fadin kasar don dakile siyen kuri'u a babbane zabe na 2019.

Lecky ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na NAN a garin Auchi, karamar hukumar Etsako ta Yamma dake jihar Edo.

“Muna kan daukar matakai don tabbatar da cewa zayyi matukar wahala ga 'yan siyasa da jam'iyu su sayi kuri'u a ranar zabe," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Firai minista Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon

Lecky ya bukaci kafafen watsa labarai da su tona asirin yan siyasa ko jam'iyyu da aka same su da siyen kuri'u a wajen gudanar da zaben, don baiwa hukumar INEC damar daukar mataki a kansu.

“Muna bukatar kafafen watsa labarai dasu tallafa mana wajen tona asirin wadanda suke siyen kuri'u don daukar mataki akansu.

"Ba zamu yanke hukunci a kansu ba, wanna aikin jami'an yan sanda ne da kotu, amma dai zamu iya samar da bayanan da za'a tuhume su da shi; rundunar 'yan sanda ce zata yi bincike a kansu," a cewar sa.

Dangane da samar da wasu rumfunan zabe, Lecky ya ce INEC zata samar da wasu rumfunan zabe bayan gudanar da zaben, domin yin hakan yanzu zai jawo cece-kuce a tsakanin 'yan siyasa.

"Ina mai tabbatarwa al'uma cewa, zaben 2019 zai kasance cikin tsafta, daga nan ne zamu iya hada bayanai da zasu bamu damar samar da karin rumfunan zabe, amma a yanzu ba zamuyi hakan ba.

"Sai dai zamu iya samar da karin akwatin zabe a wuraren da mutane sukayi yawa, wanda zai kasance ba nesa ga rumfar zaben ba, iya abinda zamu iya yi kenan, maganar samar da karin rumfunan zabe sai bayan anyi zaben 2019," a cewar sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel