A karshe : An saki matar malamin addinin nan da ‘yan bindiga suka harbe

A karshe : An saki matar malamin addinin nan da ‘yan bindiga suka harbe

- Bayan shafe kusan mako guda a hannun wadanda suka kashe mijinta, 'yan bindigar sun sake ta

- Sai dai wata majiya ta bayyana cewa an biya kudin fansa kafin sako ta

- Amma 'yan sanda sun ce ba su da masaniyar biyan kudin ga 'yan bindigar

‘Yan bindiga sun saki matar Malamin addinin da aka yi garkuwa da ita a jihar Kaduna Talatu Akuchi.

A karshe : An saki matar malamin addinin nan da ‘yan bindiga suka harbe

A karshe : An saki matar malamin addinin nan da ‘yan bindiga suka harbe

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa an saki matar ne bayan da aka biya wadanda suka yi garkuwa da ita kudi har Naira 500,000.

Talatu dai an yi garkuwa da ita ne bayan da aka kashe mai gidanta Hosea M. Akuchi kwanaki shida da suka wuce a Cocin Nasara Baptist dake yankin Guguwa, kusa da anguwar Rigasa dake jihar ta Kaduna.

Wani dan uwa wajen Talatu, wanda ba’a bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa "An sako mana Talatu ranar Asabar da daddare kuma yanzu haka tana cigaba da karbar magunguna a asibiti".

KU KARANTA: Ba zamu yarda da tsige Saraki ta karfin tuwo ba – ‘Yan fafutukar Niger Delta

"Sai da muka biya Naira dubu 500,000 kafin a sako mana ita. Kuma wannan abun Allah wadarai ne, matar da ya kamata ace yanzu tana takabar mijinta amma wanda suka kashe shi sunyi garkuwa da ita har na tsawon wajen mako guda".

‘Dan uwan nata yayi kira ga gwamnati wajen ganin ta kara zage damtse domin cigaba da kare rayuka da dukiyar al'umma.

A yayin da yake ganawa da manema labarai, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da kubutar Talatu daga hannun wanda suka yi garkuwa da ita.

Sabo ya ce "Ba mu da tabbacin an biya wasu kudade domin sakinta, amma dai mun san cewar an sake ta".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel