Buri na idan na tafi Majalisa in ga an daina barace-barace a kasar nan – Inji wani ‘Dan takara

Buri na idan na tafi Majalisa in ga an daina barace-barace a kasar nan – Inji wani ‘Dan takara

Mun samu labari cewa wani tsohon ‘Dan Majalisar wakilan Tarayya da ya taba wakiltar wani Yanki na Arewacin Kasar nan yace babban burin sa shi ne ya ga an daina bara idan ya koma Majalisar kasar.

Buri na idan na tafi Majalisa in ga an daina barace-barace a kasar nan – Inji wani ‘Dan takara

Aliyu Gebi yana neman kawo kudirin hana bara a Najeriya

Honarabul Aliyu Ibrahim Gebi wanda ya taba wakiltar cikin Garin Bauchi a karkashin Jam’iyyar CPC yana neman komawa Majalisar Tarayyar a zaben 2019. Gebi yace idan har Allah ya ida nufin sa, zai dage wajen ganin an haramta bara.

Ba nan kadai tsohon ‘Dan Majalisar ya tsaya ba, ya kuma yi alkawarin cewa zai yi bakin kokarin sa wajen ganin ‘Ya ‘ya mata sun samu ilmi a saukake a Kasar nan. Hon. Gebi yace kuma zai zama mai jin kukan mutanen Mazabar na sa.

KU KARANTA: Yadda wasu Gwamnoni su ka hada karfi-da-karfi wajen lashe kujerar Sanata a Bauchi

Kamar dai yadda ‘Dan siyasar ya bayyana a shafin sa na Tuwita zai kuma dage wajen ganin an daina amfani da talaucin jama’a wajen bautar da su. Aliyu Gebi yace haka kuma zaiyi kokarijn ganin an daina yaudarar mutane ta fuskar kabilaci.

Bugu da kari kuma yace zai kawo kudirin da zai hana maida yara boyi-boyi da ake yi da sunan Almajiranci wanda ya zama annoba musamman a Arewacin Najeriya. Kwanaki dai Gebi ya fito takarar Sanatan Bauchi ta Kudu amma ya janye.

Aliyu Ibrahim Gebi wanda ya taba zuwa Majalisa a 2011 zuwa 2015 yanzu yana cikin masu ba Ministan harkokin cikin gida watau Janar Abdulrahman Dambazzau shawara. Gebi yana da kokarin taimakawa marasa karfi musamman yara kanana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel