Ina nan a Jam’iyyar mu ta PDP daram-dam-dam – Inji Atiku

Ina nan a Jam’iyyar mu ta PDP daram-dam-dam – Inji Atiku

Mun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Alhaji Atiku Abubakar yayi magana game da rade-radin ficewar sa daga Jam’iyyar adawa ta PDP. Atiku yace babu burbushin gaskiya a lamarin domin ba zai yi watsi da jan aikin da ya fara ba.

Ina nan a Jam’iyyar mu ta PDP daram-dam-dam – Inji Atiku

Atiku yayi magana game da batun barin PDP

Kamar yadda labari ya zo mana a cikin karshen makon da ya gabata, ofishin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya karyata maganar cewa ‘Dan takarar Shugaban kasar ya fice daga PDP. Kwanan nan dai ne aka fara wannan jita-jita a kasar.

Mun samu wani jawabi da ya fito daga Ofishin AMO wanda ke taya tsohon Mataimakin Shugaban kasar yakin neman takara inda aka bayyana cewa rade-radin banza ne kurum ake yadawa domin kawowa ‘Dan takarar cikas a zaben 2019.

Atiku Abubakar din na nan a Jam’iyyar PDP kuma yana cikin sahun-gaba na masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawar a zabe mai zuwa inda aka kara tabbatar da cewa a shirye Atiku yake da ya karbi mulki.

KU KARANTA: Kwankwaso zai nemi ya kara da Shugaban Kasa Buhari

Cikin watanni 2 da su ka wuce, ‘Dan takarar dai yana ta cigaba da zagaye kasar nan domin samun goyon bayan manyan ‘Yan PDP a zaben fitar da gwanin da za ayi. Atiku na cigaba da tallata kan sa a matsayin ‘Dan takarar da ya fi cancanta a PDP.

Jawabin ya kuma nuna cewa Atiku zai yi takaran neman tikitin PDP babu tantama sannan kuma ya nemi doke Shugaban kasa Buhari a shekara mai zuwa. AMO tace don haka hankali ma ba zai dauka ba idan aka ce Atiku ya bar PDP a yanzu.

Kwanan nan ku ka ji cewa an yi ca a kan Atiku bayan ya soki Shugaba Buhari. Kalaman Atiku sun jefa sa cikin matsalar da bai yi tunani ba inda Jama’a su kayi ta sukar sa a Tuwita. Atiku ya caccaki Gwamnatin Buhari ne kan watsi da harkar lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel