Jam’iyyar APC ta maidawa Saraki martani bayan yace bai tsoron a tsige sa

Jam’iyyar APC ta maidawa Saraki martani bayan yace bai tsoron a tsige sa

Labari ya iso gare mu cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta kalubalanci Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bude Majalisa idan har ba ya gudun Sanatoci su tsige sa daga kujerar sa kamar yadda yake fada.

Jam’iyyar APC ta maidawa Saraki martani bayan yace bai tsoron a tsige sa

Ana cigaba da maidawa juna kalamai tsakanin Saraki da APC

Jaridar Punch ta rahoto cewa Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta bakin Sakataren yada labarai Yekini Nabena ta maidawa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki amsa bayan yace sam bai gudun a cire sa daga kujerar sa.

Yekini Nabena wanda shi ne Sakataren yada labarai na APC na rikon kwarya ya fadawa ‘Yan jarida idan har Bukola Saraki yana ji ya isa, ya bude Majalisar ya gani ko za a iya tsige sa tare da bin dokar kasar nan ko kuma ba za a iya ba.

KU KARANTA: Ko a jiki na: Ba na damun kai na game da barazanar tsige ni a Majalisa – Saraki

Nabena wanda yake rike da kujerar a matsayin rikon kwarya yace hankali kwance za a tsige Saraki sannan kuma a ba wani cikakken ‘Dan Jam’iyyar APC mukamin. Jam’iyyar tace tun da Saraki ya koma PDP, babu yadda za ayi ya rike mukamin sa.

Sanatocin APC dai sun nuna cewa babu dalilin PDP wanda ba ta da rinjaye ta cigaba da rike shugabancin Majalisar. Jam’iyyar APC dai tace tana tare da Sanatocin ta a kan wannan batu inda ta sha alwashin yin waje da Saraki daga kujerar.

Dama kun san cewa Shugaban Majalisar Dattawa yace sam ba ya jin dar-dar din a cire sa daga matsayin sa domin kuwa dokar kasa tayi tanadin abin da ya kamata. Saraki ya bayyana wannan ne a Garin Asaba lokacin da ya gana da Gwmnan Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel