Hadimin Buhari na bogi ya damfari masu neman aiki 14 a Niger

Hadimin Buhari na bogi ya damfari masu neman aiki 14 a Niger

- Rundunar yan sandan jihar Niger sun kama wani dan shekara 37 bayan ya badda kamanni a matsayin hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen damfarar wasu masu neman aiki

- Bisa ga yan sanda, mai laifin, Kabiru Mohammed ya damfari masu neman aiki 14

- Ya damdari mutanen sama da naira miliyan 4.2

Rundunar yan sandan jihar Niger ta kama wani mutumi mai sauya kama a matsayin hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin damfarar wasu masu neman aiki sama da naira miliyan 4.2.

An zargi Kabiru Mohammed mai shekaru 37 da damfarar wasu masu nean aiki 14 a ynkin karamar hukumar Gurara.

An tattaro cewa mai laifin ya yaudari mutanen ne ta hanyar fada masu cewa uangidansa, wadda a cewarsa daya daga cikin hadiman shugaban kasa ne yana da hanyar nema masu aiki a hukumomin yan sanda, kwastam, NSCDC, sojin ruwa, sojin sama da kuma kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).

Hadimin Buhari na bogi ya damfari masu neman aiki 14 a Niger

Hadimin Buhari na bogi ya damfari masu neman aiki 14 a Niger

Wadanda aka damfara Atahiru Tukura, Bello Abubakar, Mohammed Hussaini, Rabiu Tukura, Umar Danladi, Jibrin Shagabe, Zubairu Danladi, Halidu Musa, Basiru Usman, Mustaph Shehu, Ibrahim Mustaph, Yusuf Ibrahim, Adamu Mohammed da kuma Ahmed Salihu sunce sun biya Muhammed tsakanin N100,000 da N800,000.

Yan sandan sun kama Ishaya Christopher isa zargin buga takardan daukar aiki da katunan shaida na bogi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC

Yan sanda sun bayyana cewa Mohammed yace ya kasance na tsakiya ne tsakanin uangidansa da ba’a bayyana sunansa bad a wadanda aka damfara.

Yace tsakani da Allah shi bai san damfara bane domin mutane da dama sun samu aiki ta ayan fage a Najeriya.

Kakakin yan sandan Muhammad Auakar yace mai laifin ya amsa laifinsa cewa sun aikata hakan tare da Peter James wadda a yanzu ya ci kafar kare.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel