Bayan an kashe soja daya, jami’an soji sun kai mumunan farmaki garin Abua a jihar Rivers

Bayan an kashe soja daya, jami’an soji sun kai mumunan farmaki garin Abua a jihar Rivers

Mutan garin Abua da ke jihar Rivers sun waya gari cikin fargaba da tsaro yayinda jami'an hukumar sojin Najeriya suka far musu kan don fanshe kisan wani abokin aikinsu a garin.

Jami’an sojojin Najeriya a ranan Asabar, 25 ga watan Agusta sun kai farmaki garin Abua, karamar hukumar Abua-Odual na jihar Rivers bisa ga kisan dan uwansu da akayi a garin.

Jaridar Sauthern City News ta bada rahoton cewa an kashe jami’an soja daya, jami’an dan sanda daya, da wani mai farin hula yayin yunkurin garkuwa da wasu turawa biyu da ke aiki a wani kamfanin man fetur.

An tattaro cewa jami’an sojoji sun mayar da wannan martini ne da sanyin safiya inda sukaci mutuncin mazauna garin kuma suka tare hanyoyin shiga da fita a garin.

KU KARANTA: Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure

Wani matashi daga garin Omelema wanda aka sakaye sunansa ya ce jami’an soji sun damke mazauna garin kun sun kora wau.

Yace: “Na yi mamakin ganin sojoji ko ina; wasu sun damke masu babur tare da baburansu. An tilasta wasu zama a kasa – manya da yara.”

Wata majiya daban tace bayan sun kwace sakatariyar karamar hukumar, sun koma karamar hukumar Okpeden in aka kashe dan uwansu.

Amma bayan sa’ao’I kalilin misalin karfe 10:15 na safen, sojoji sun saki dukkan waanda suka kama kuma suka tafi.

Da aka tuntubi kakakin barikin sojin Division 6 na hukumar soji, Kanal Aminu Iliyasu, ya ce tunda baya gari, bai da masaniya game da farmakin amma zai yi magana anjima.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel