Shegiyar uwa: Wata mata ta sayar da jaririyarta, ta sayi waya da kudin

Shegiyar uwa: Wata mata ta sayar da jaririyarta, ta sayi waya da kudin

- Talauci ya tilasta wata mata sayar da sabuwar jaririyarta

- Amsan kudin ke da wuya, sai ta garzaya shagon waya

Jami’an hukumar yan sandan jihar Edo sun zurfafa bincike cikin wani al’amarin ban mamaki da ban takaici inda wata mata mai suna Miracle Johnson ta sayar jaririyarta yar makonni shida kacal a haihuwa a jihar.

Kwamishanan yan sandan jihar, Mr Johnson Kokumo, wanda ya tabbatar wannan labari ya bayyanashi a matsayin babban laifi.

Jaridar Punch Metro ya tattaro cewa Miracle Johnson ta sayar da jaririyar mai suna Greatness ga wani gidan marayu da ke garin Onitsha na jihar Anambra a kudi N200,000.

Miracle Johnson yar asalin Agenebode, karamar hukumar Etsako East na jihar Edo ta amshi kudin nakadan kuma ta kama gaba ta sayi wayan tarho.

KU KARANTA: Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

Da asiri ya tonu, Miracle ta daura laifin wannan abun kunya da tayi kan gazawar maigidanta na kula a ita sauran yaranta guda biyu.

Ta kara da cewa wata mata mai suna Mama Joy ce ta bata wannan shawara ta sayar saboda su samu kudin kasuwanci tare a mijinta.

Tace: “An haifi jaririyata rana 2 ga watan Yuli. Na sayar da ita ne saboda tsananin talauci. Mijinta wahalla yake yi domin ciyar da mu.”

“Kawata (Mama Joy) ta shawarceni cewa tun da mijinta ya gaza kula dani, in sayar da jaririyar sai in baiwa mijina kudin ya fara kasuwanci da shi ko ya sayi babur.”

“Na sayar da ita ga wani gidan marayu a Onitsha. Gidan marayun sun saya a kui N200,000. Waya kadai na sayi; ban son siya amma Mama Joy ta tilasta ni”

Wannan abu bai yiwa Miracle dadi ba, sai ta kai karan kanta wajen Fasto.

Mijinta mai suna Johnson Omovuokpor, ya bayyana rashin dadinsa kan wannan abu da matarsa tayi duk da cewa ya ki hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel