2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC

2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC

- Ga dukkan alamu ba'a gama warware rikicin APC a jihar Kaduna ba

- Jigon jam'iyyar a Kaduna ya bayyana cewa babu wani tikiti da za'a ba Shehu Sani da sauransu kai tsaye kamar yadda ake yayatawa

- A cewar Ibrahim jam'iyyar na da tsari da kundin mulki da ake bi

- Ya kuma jadadda cewa Shugaba Buhari da Oshiomhole asu tsayar da Shehu Sani a matsayin dan takarar majalisar dattawa a jihar ba

Rikicin da ake fama dashi kan dakatar da sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani da kuma wanda zai samu tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a wannan yankin na kara kamari.

Mataimakin sakataren shiri na jam’iyyar APC, Hon. Muhammad Sani Ibrahim a jiya ya kaddamar da cewa babu wani mutum da zai iya ba kowani mamba tikitin jam’iyyar kai tsaye.

Ibrahim wadda ya kasance tsohon mamba a majalisar wakilai daga jihar Kaduna, yayi kira ga ýan Najeriya da kuma mambobin jam’iyyar da suyi watsi da raderadin bayar da tikiti kai tsaye ga Sanata Shehu Sani da wasu sanatoci daga yankin arewa maso yamma.

2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC

2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC

A wata sanarwa da aka gabatar ga manema labarai a jihar Kaduna a jiya, Lahadi, 26 ga watan Agusta, Ibrahim ya bayyana irin wannan rade-radin dake yawo a gari a matsayin abun damuwa.

KU KARANTA KUMA: Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

Ibrahim ya kuma bayyana cewa rade-radin da ake yin a cewa Shugaban kasa Muhammadu uhari da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole sun tsayar da Sani a matsayin mai neman kujerar majalisar dattawa a 2019 a gaskiya ane, inda ya jadadda cewa akwai tsayayyen tsari dxa kundin tsarin mulkin jam’iyya da ake bi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel