Kasar Amurka ta ce an samu karuwar cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari

Kasar Amurka ta ce an samu karuwar cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari

- Kasar Amurka ta ce cin hanci da rashawa yayiwa Nigeria katutu

- Rashin gurfanar da masu laifi gaban shari'a ne ya kawo hakan

- Amurka ta lissafa cin zarafin 'yancin bil Adama da ake yi a Nigeria

Rahoton da kasar Amurka ta fitar ya ce gazawar shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari na kaddamar da hukuncin shari'a ga wadanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa ne ya jawo lamarin cin hancin yayiwa kasar katutu.

A rahotonta na 2017 kan 'yancin dan Adam, Amurka ta ce an samu rahotannin cin hanci da rashawa a kowane mataki na gwamnatin kasar.

Ta kara da cewa: "Duk da cewa doka ta bayyana hukuncin da za'a yanke ga wadanda suka ha'inci kasarsu da aikinsu, gwamnatin Buhari ta gaza bin wannan doka ta yadda ya dace, hakan ya sa manyan jami'an gwamnati ke cin hanci da rashawa yadda suke so.

"Akwai yaduwar almundahana a kowane matakin gwamnati na kasar, ciki kuwa harda fannin tsaro. Sai dai, doka ta bada kariya ga shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni da mataimakansu, ma damar suna akan mulki, ba zasu fuskanci shari'a ba," a cewar kasar Amurka.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Rundunar 'yan Sanda ce ta tilasta Jonathan amincewa da sakamakon zaben 2015

Rahoton da kasar ta fitar, ya kara da cewa, a yayin da hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ke gudanar da bincike, hukumar ta gaza bin hanyoyin da suka dace wajen kawo karshen hakan a kasar.

Rahoton ya buga misali da shari'ar Sambo Dasuki, tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa kan fannin tsaro, wanda ya ke garkame a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS tun 2015, yana mai cewa anyi biris da umarnin kotu na sallamar Dasuki.

Amurka ta lissafa wasu manyan bayanai da suka faru a wannan shekarar, na tauye hakkin bil'adama, da suka hada da: "Daukar tsattsauran hukunci da kashe kashen ba gaira babu dalili; bacewar mutane da tsaresu babu shari'a.

"Akwai zabtarwa, musamman a gidajen da ake tsare da mutane, da suka hada da cin zarafin 'yaya mata da yi masu fyade; amfani da kananan yara a harkokin tsaro, damfara, da kuma lalata kayayyaki; tsare fararen hula a magarkamar jami'an soji, kawai saboda wasu dalilai marasa tushe"

Har ila yau, ta ci gaba da lissafa abubuwan da suka farun, da cewa: "Akwai kin baiwa mai laifi damar zuwa kotu; yin karantsaye ga fannin shari'a; tauye hakkokin jama'a; tauye 'yancin fadar albarkacin baki, musamman ma ga 'yan Jarida; cin hanci a tsakanin manyan jami'ai; karancin bincike kan kararraki da suka shafi mata da kananan yara; safarar mutane da yiwa mata auren wuri da na dole."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel