Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

- Gwamna Samuel Ortom na shirin fadawa a taken ta leko ta koma

- Hakan ya iyo bayan yan takarar kujerar gwamnan jihar Benue karkajin PDP 12 da suka ce bazasu janye masa ba

- Sun gargadi shugaban jam'iyyar kan cewa kada yayi yunkurin tsayar da Ortom domin sune suka tsaya tsayin daka a jam'iyyar lokacin da ya fice ya koma APC

- Gwamna Ortom dai ya nuna ra'ayinsa na son yin tazarce

Dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Benue, Dr Tivlumun Nyitse, ya bayyana abunda ya wakana tsakanin Gwamna Samuel Ortom da sauran yan takarar gwamna a jam’iyyar a wata ganawa da akayi.

Nyitse yace tara daga cikin 12 naa mamoin PDP a jihar Benue wadanda ke sanya ran zamowa gwamnan jihar a 2019 sun hadu da Ortom, wanda ya sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyar a kwanakin baya, kuma yana neman a ashi tikitin sake tsayawa a takara na jam’iyyar.

Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

A cewar Nyitse, Ortom ya fadama yan takarar kujerar gwamnan cewa yana son yin tazarce.

Yace yayinda sauran yan takarar suka yiwa Ortom maraba da dawowa jam’iyyar, sun gargadi shugaban jam’iyyar kan kada yace zai tsayar da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

Cewa ya zama dole jam’iyyar ta tuna cewa yan takarar 12 sun jajirce a jam’iyyar lokacin da Ortom ya fice ya koma jam’iyyar adawa.

Sunce a zai yiwu gwamnan yaci a jam’iyyar da ya aro sannan ya sake ci anan ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel