Sauyin sheka: Wani sanatan PDP na shirin komawa jam'iyyar APC

Sauyin sheka: Wani sanatan PDP na shirin komawa jam'iyyar APC

- Sanata Buruji Kashamu na shirin komawa jam'iyya mai mulki ta APC

- Sanatan yana wakiltar al'ummar jihar Oyo ne

- Jam'iyyar PDP ce ta kore shi tun farko

Mun samu labarin cewa daya daga cikin 'yan majalisar dattawan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a Najeriya dake wakiltar jihar Ogun shiyyar gabas watau Sanata Buruji Kashamu na shirin komawa jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan dai kamar yadda muka samu labari yana da nasaba ne da korar sa da jam'iyyar ta PDP tayi sakamakon laifuffukan da ya tafka a cikin jam'iyyar.

Sauyin sheka: Wani sanatan PDP na shirin komawa jam'iyyar APC

Sauyin sheka: Wani sanatan PDP na shirin komawa jam'iyyar APC

KU KARANTA: Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita tsadar aure

Legit.ng ta samu cewa sai dai a nasu bangaren wata kungiyar masu rajin kare muradun jam'iyyar ta APC a jihar watau Ogun Youth Consultative Vanguard a turance sun gargadi jam'iyyar akan karbar Sanatan domin kuwa a cewar su matsala kawai zai jaza masu.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya tace tana kalubalantar jam'iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa ga wata muhawara ta keke-da-keke.

Jam'iyyar ta PDP haka zalika ta ce manufar yin hakan shine domin su tattauna akan al'amurran da suka shafi yau da kullum da kuma harkokin mulkin kasar ta yadda al'umma masu zabe za su tantance inda aka dosa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel