Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

- Yan sandan jihar Imo sun kama wani gawurtaccen dan kungiyar asiri kuma makashi

- A cewar mai laifin mutane uku kawai ya kashe tunda ya shiga kungiyar asiri a 2014

- Dama dai yan sanda sun dade suna farautarsa har dai suka yi nasarar cafke shi a ranar 19 ga watan Agusta

Jami’an yan sandan dake yaki da fashi da makami a jihar Imo sun kama wani gawurtaccen dan kungiyar asiri kuma makashi, Chijioke Ogbonna wadda aka fi sani da Ogotiti.

Yayinda yan sanda suka gurfanar da shi a ranar Asabar da ya gaata, Ogotiti ya fadama manema labarai cewa ya kashe mutane uku tunda ya shiga kungiyar asiri a shekarar 2014.

Matashin mai shekaru 23 wanda ya kasance dan makarantar Federal Polytechnic, Nekede, yace kudirin da ya dauka na daukar fansa ne ya kai shi ga kashe mutane uku, daya daga cikinsu ya kasance dan kungiyar adawarsu.

Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

Mutane 3 kawai na kashe tunda na shiga kungiyar asiri – Dan makaranta

Ogbotiti wadda ya kasance dan asalin garin Umuejije, karamar hukumar Isialangwa ta kudu dake jihar Abia yayi bayanin cewa babban makami da yake amfani da shi ya kasance bindigar gargajiya.

KU KARANTA KUMA: Tantiran tsagerun Neja Delta sun yi barazanar dagulawa Shugaba Buhari lissafi

Jami’in hulda da jama’a na rundunaar yan sandan jihar Imo, Andrew Enwerem ya bayyana mai laifin a matsayin gawurtaccen dan kungiyar asiri da fashi da makami, ya kara da cewa jami’an SARS ne suka kama shi a ranar 19 ga watan Agusta a Ama-Hausa dake yankin Owerri, babban birnin jihar.

Enwerem yace yan sanda na neman mai laifin tun a 2014 kan zargin rawar ganin da yake takawa wajen aikata ayyukan laifi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel