Babban kashi: Kwankwaso zai kara da Buhari a zaben 2019

Babban kashi: Kwankwaso zai kara da Buhari a zaben 2019

- Shirye-shiryen zaben 2019 na cigaba da kankama

- 'Yan takarkaru daga jam'iyyu daban-daban na bayyana hajar da suke dauke da ita

Gabanin bayyana shirinsa na takarar shugabancin kasa a ranar Laraba mai zuwa, Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano wato Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya bara, inda ya bayyana cewa kasar nan ta rasa ababen more rayuwa.

An zo wurin: Kwankwaso ya ya bayyana dalilin yin takararsa a 2019

An zo wurin: Kwankwaso ya ya bayyana dalilin yin takararsa a 2019

Cikin wata sanarwa mai dauke da bayanin yadda za'a gudanar da tsare-tsaren bikin kaddamar da takarar, ya bayyana cewa bashin da ake bin kasar nan ya kai intiha.

Sanata Kwankwaso wanda sau biyu yana zama gwamnan jihar Kano zai fafata da jiga-jigan 'yan siyasar dake neman PDP ta tsayar da su takara a zaben 2019.

Cikin mutanen dake burin jam'iyyar ta ba su damar yin takarar shugabancin kasar har da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da takwaransa na jihar Kaduna, Ahmed Makarfi da tsohon Ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki da kuma takwaransa na Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau.

KU KARANTA: Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

Da alama duk wanda PDP ta tsayar a zaben 2019 zai fafata da Shugaba Buhari, wanda masu sharhi a fannin siyasa ke ganin shi APC za ta tsayar a zabe mai zuwa tunda ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Kwankwaso ya bayyana cewa, “Alhakinmu ne wajen ganin mun magance matsalar da kasar nan ta ke fuskanta a bangarorin abubuwan more rayuwa da kuma yadda bashi daga kasashen ketare ke kara yiwa kasar nan katutu".

Ya kara da zai magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan a duk lungun da sako dake fadin kasar nan.

A karshe sanarwar ta ce idan aka yi la'akari da yadda tsohon gwamnan jihar Kanon ya kawo aiyukan raya kasa da bunkasar tattalin arzikin jihar Kano, wannan kadai ya isa zama shaidar cewa zai iya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel