Akwai kwantaciyyar rikicin Boko Haram a Najeriya inji wani babban Jami’in DSS

Akwai kwantaciyyar rikicin Boko Haram a Najeriya inji wani babban Jami’in DSS

Mun samu labari daga wadanda su ke filin daga cewa rikicin Boko Haram na nema ya zama danye. Yanzu haka dai ‘Yan ta’addan su na cigaba da kara karfi a Yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Akwai kwantaciyyar rikicin Boko Haram a Najeriya inji wani babban Jami’in DSS

Idan aka yi sake yakin Boko Haram zai dawo sabo - Rahotanni

Wani babban Jami’in DSS wanda ya dauki shekara da shekaru a inda ‘Yan ta’addan Boko Haram ke barna ya bayyana cewa rikicin ya wuce yadda ake tunani. Jami’in na DSS yace har yanzu ba a kama hanyar gamawa da Boko Haram ba.

Kamar yadda labari ya zo kunnen NAIJ Hausa, wannan babban Jami’in DSS din ya bayyana cewa akwai ‘Yan ta’adda makil a irin su Yankin Yunusari a cikin Jihar Yobe. Haka kuma akwai dubunnan ‘Yan ta’addan na Boko Haram a cikin Jihar Borno.

KU KARANTA: Abin da ya sa Jonathan ya saduda - Tsohon Shugaban 'Yan Sanda

Wannan Jami’in tsaron da ba zai so a bayyana sunan sa ba yake cewa ‘Yan Boko Haram din su na nan a Yankin Munguno da kuma Guzamal, da Kukawa da Marte da wasu Yankin na Borno. Sojojin kasar na ikirarin cewa an samu zaman lafiya a Yankin.

Tun a baya dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun gama lallasa ‘Yan ta’addan Boko Haram. Sai dai yanzu abubuwa sun nuna cewa har yanzu akwai sauran aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel