Wasu masu rike da madafan iko sun nemi Buhari ya kori Magu da Munguno

Wasu masu rike da madafan iko sun nemi Buhari ya kori Magu da Munguno

Labari ya zo mana cewa an hurowa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wuta ya tsige Mai ba sa shawara kan harkokin tsaro watau NSA da kuma Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC.

Wasu masu rike da madafan iko sun nemi Buhari ya kori Magu da Munguno

Ana neman Buhari ya kori Shugaban EFCC daga aiki

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu manya a cikin Gwamnatin Buhari sun fara kiran a kori Birgediya Janar Babagana Munguno (mai ritaya) daga matsayin sa na mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Najeriya.

Bayan nan kuma ana neman tursasa Shugaban kasar yayi waje da Ibrahim Magu wanda shi ne Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa bayan sallamar Shugaban Hukumar DSS.

Hakan na zuwa ne bayan Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tsige Lawal Daura daga aiki. Wasu wanda Shugaban kasar yake ji da su sun nuna masa dalilan da su ka sa ya dace a kori manyan masu rike da sha’anin tsaro na kasar.

KU KARANTA: An sace miliyoyin kudi a wani asibiti a Garin Borno

Ana tunanin cewa an kori Lawal Daura daga aiki ne domin irin su Magu da Munguno su zauna lafiya, hakan ta sa ake nema Shugaban kasar ya kori kowa domin a huta. Sai dai kuma wasu a Gwamnatin su na neman a bar su Magu a ofis.

Kamar yadda labarin yake zuwa mana, wani Gwamna a Kasar Yarbawa ne ke hurowa Shugaban kasa Buhari wuta ya sallami Magu. Ana zargin cewa Gwamnan yana da alaka da wasu da Hukumar EFCC ke zargi da laifin tafka sata a Gwamnati.

Wasu manyan Arewa da ke Gwamnatin nan su na jin haushin yadda Shugaban kasar yake alaka da wasu daga Arewa maso Gabashin Kasar. Dama dai Tsohon Shugaban DSS Daura yana cikin wadanda su ka hana a tabbatar da Magu a EFCC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel