Gwamnan PDP ya sha yabo saboda biyayyar da yake yiwa Buhari

Gwamnan PDP ya sha yabo saboda biyayyar da yake yiwa Buhari

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya bayyana jin dadi tare da yaba wa gamnan jihar Enugu, Ifeanyi Uguanyi, saboda girmama shugaba Buhari.

Kalu ya bayyana cewar Uguanyi na bawa shugaba Buhari girma na musamman da ya wuce irin na ragowar 'yan siyasa.

Kazalika, Kalu, ya bayyana cewar shugaba Buhari na matukar ganin girman gwamna Uguanyi.

Gwamnan PDP ya sha yabo saboda biyayyar da yake yiwa Buhari

Gwamnan PDP ya sha yabo saboda biyayyar da yake yiwa Buhari

Kalu na wadannan kalamai ne a fadar gwamnatin jihar Enugu yayin wata ziyara da ya kaiwa gwamna Uguanyi, kamar yadda jaridar Times ta rawaito.

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

"Akwai kyakykyawar fahimtar juna tsakanina da Uguanyi, tun kafin ya zama gwamna kuma na sha fada wa shugaba Buhari yadda banbancin siyasa bai shafi mu'amalar mu ba," a kalaman Kalu.

Sannan ya kara da cewa, "hatta shugaba Buhari na daukan Uguanyi a matsayin dan cikin gida duk da kasancewar sa dan jam'iyyar PDP. Uguanyi bai taba sukar Buhari ba."

Kazalika, Kalu ya karyata rahotannin dake yawo a gari cewar yana shirin komawa jam'iyyar PDP tare da alakanta hakan da aikin wasu wasu da ya kira makiyansa na siyasa.

Kalu ya kare jawabinsa da cewar gara ya hakura da siyasa bakidaya a kan ya shiga jam'iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel