An kama masu gadin da suka sace Naira Miliyan N5m a wani asibitin jihar Borno

An kama masu gadin da suka sace Naira Miliyan N5m a wani asibitin jihar Borno

- Son abin Duniya ya kai wasu masu aikin gadi ya baro

- Zuciyarsu ta yaudare su sun saci makudan kudade a wurin aikinsu

- Sai dai tuni 'yan sanda suka zabaro su bayan sun kashe kudaden

Jami'an rundunar ‘yan sanda ta SARS sun kame wasu masu aikin gadi bisa zarginsu da sace kudi kimanin Naira miliyan biyar a asibitin kwararru dake Maiduguri.

An kame masu gadi bisa zargin sace Naira Miliyan N5m a wani asibiti a jihar Borno

An kame masu gadi bisa zargin sace Naira Miliyan N5m a wani asibiti a jihar Borno

Wata majiya mai karfi ta bayyanawa kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) cewa an kame wadanda ake zargin ne ranar Asabar, sakamakon binciken da jami'an tsaro suka gudanar.

Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa barayin sun samu nasarar sace kudin ne ta hanyar shiga ofishin ma’ajin kudi ta saman rufin kwanon, inda ta nan suka sace makudan kudin.

“Bayan sun sace kudin sun sayo Mota ta sama da Naira miliyan biyu, tare kuma da garzayawa jihar Kano inda suka kashe kudin. Bayan da su ka batar da kudin ne, sai suka sayar da motar".

Da ya ke tofa albarkacin bakin sa akan faruwar lamarin shugaban asibitin Dakta Laraba Bello, ya ce barayin da suka yi wannan satar masu Gadin su ne.

KU KARANTA: Kisan wani dalibi ya jefa jami’in SARS cikin chakwakiya

“Ranar daya ga watan Mayu, ma’ajin kudin asibitin ya zo aiki, kawai sai ya tarar da ma'ajiyar kudi a karye, amma kuma kofar a rufe take".

Ya kara da cewa wannan al'amarin ya jefa ma'aikatan asibitin cikin firgici da tashin hankali

A nasa bangaren shugaban kamfanin samar da masu gadi na HIM Global Nigerian Security Mista Babatunde Satomey, ya bayyana cewa tuni kamfanin ya dauki matakin korar wadanda suka aikata laifin.

“Gaba dayansu mun sallamesu daga bakin aiki, domin sabawa dokar aiki da suka yi"

A karshe ya tabbatar da cewa sun hada kai da rundunar tsaron ta farin kaya , DSS da Sojoji domin aiki tare da cigaba da samar da amintattun gadi, tare da bankado baragurbin.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel