Asiri ya tonu: Rundunar 'yan Sanda ce ta tilasta Jonathan amincewa da sakamakon zaben 2015

Asiri ya tonu: Rundunar 'yan Sanda ce ta tilasta Jonathan amincewa da sakamakon zaben 2015

- Rundunar ‘yan sanda ta yi ikirarin cewa itace ta tilasta Jonathan amincewa da sakamakon zaben 2015

- Tsohon sifeta janar na rundunar ya ce sune ya kamata a kira Gwaraza a zaben na 2015

- Ana kallon Jonathan a matsayin Jarumin siyasa wanda ya amince da sakamakon zabe da kuma taya Buhari murnar samun nasara

Tsohon Sifeta Janar na rundunar ‘yan sanda, Suleiman Abba ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandace ta tilastawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyar PDP amincewa da sakamakon zabe, da kuma kiran Buhari don taya shi murnar lashe zaben.

Sulaiman yayi ikirarin cewa ya shiga halin tsaka mai wuya a wajen kusoshin jam’iyar PDP na yin murdiya a zaben 2015 da ya gabata.

KARANTA WANNAN: Munsha azaba a hannun DSS tsawon shekaru biyu -Clinton

“Mun godewa Allah daya zamana cewa zamu iya tilasta wadanda suka sha kasa a zabe amincewa da sakamakon zaben. Rundunar ‘yan sanda na tilastawa wadanda suka sha kayi su amince da sakamakon da hukumar INEC ta fitar.

“A nan ina Magana ne akan Rundunar ‘yan sanda, ba wai kokarin kashin kaina, ni Suleiman Abba ba. Duk abubuwan da suka faru ya ta’allaka ne akan namijin kokarin da rundunar ta yin a tilasta su amincewa da sakamakon zaben da aka fitar. ‘Yan sanda ne ya kamata a kirasu gwarazan wannan zabe” a cewar sa, cikin wata hira da yayi da Daily Trust.

An dai yabawa tsohon shugaban kasa Jonathan bisa amincewa da sakamkon zaben 2015, tare da kuma kiran wanda ya ci zabe a lokacin (Buhari) don taya shi murna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel