Guguwar canji: Hadiman wani gwamnan PDP sun koma APC da mutane fiye da 5,000

Guguwar canji: Hadiman wani gwamnan PDP sun koma APC da mutane fiye da 5,000

Wasu masu taimakawa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, sun ja zugar mutane fiye da 5,000 zuwa jam'iyyar APC.

Masu taimaka gwamnan su biyu sun bayyana ficewar su daga jam'iyyar PDP ne a jiya, Asabar, yayin kaddamar da takarar tsohon hukumar tattarar haraji a jihar Delta, Onowakpo Thomas, dake neman jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isoko.

Yayin kaddamar da takarar ne mataimakan gwamnan biyu; Lucky Arumare da Uyoyou Edhekpo, suka bayyana fitar su daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayansu fiye da 5,000.

Guguwar canji: Hadiman wani gwamnan PDP sun koma APC da mutane fiye da 5,000

Guguwar canji: Hadiman wani gwamnan PDP sun koma APC da mutane fiye da 5,000

A jawabin shugaban jam'iyyar APC a jihar ta Delta, Jones Erue, ya bayyana cewar zasu fitar da gwamna Okowa daga gidan gwamnati a 2019.

DUBA WANNAN: 2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

A jiyan ne dai tsohon gwamnan jihar ta Delta, Emmanuel Oduaghan, ya bayyana ficewar sa daga jam'iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki.

Komawar Oduaghan APC ta kawo adadin tsofin gwamnonin PDP da suka fita ya zuwa biyu.

Ranar 8 ga watan Agusta ne aka yi bikin karbar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Godswil Akpabio, zuwa jam'iyyar APC bayan ya bayyana fitar sa daga PDP ranar 2 ga watan na Agusta.

Jam'iyyar APC na fatan ganin ta karya karfin da PDP ke da shi a yankin kudu maso kudu na tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel