Hadimin gwamnan Kwara yayi murabus, ya ki binsa PDP

Hadimin gwamnan Kwara yayi murabus, ya ki binsa PDP

- Wani shuhada'un APC ya gwammace ajiye mukaminsa da ya bi gwamnan jiharsa PDP

- Gwamnan jihar Kwara da shugaban majalisar APC duk sun sauya sheka amma yaki binsu

- Sai dai ya bayyana godiyarsa da damar da ya samu ta hidimtawa jama'ar jihar

Abdullahi Danbaba mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara kan harkokin da basu shafi gudanar da gwamnati ba ya sauka daga mukaminsa don cigaba da zama a cikin jam’iyyar APC.

Hadimin gwamnan Kwara yayi murabus yaki binsa PDP

Hadimin gwamnan Kwara yayi murabus yaki binsa PDP

Danbaba ya sanar da sauka daga mukamin nasa ne ta hanyar wasikar da ya aikewa gwamnan jihar wadda kuma kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya samu kwafinta, a yau Lahadi a garin Ilorin.

Ya bayyana cewa yin murabus din nasa ya biyo bayan tuntubar makusantansa da ragowar mutanen mazabarsa da ma na jihar ta Kwara.

KU KARANTA: 2019: Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayar da ta dauka a kan fitar da dan takara

Daga nan ne ya godewa gwaman jihar Abdulfatah Ahmed da shugaban majalisar wakilai ta kasa Bukola Saraki bisa damar hidimtawa al’ummar jihar da ya samu.

Wannan murabus na Danbaba shi ya mayar da adadin mutanen da suka sauka daga mukamin nasu zuwa biyu a jihar tun bayan sauya shekar gwamnan zuwa PDP.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel