2019: Za a yi wata muhimmiyar ganawa tsakanin Buhari da shugabannin APC na kasa da jihohi

2019: Za a yi wata muhimmiyar ganawa tsakanin Buhari da shugabannin APC na kasa da jihohi

A yau ne shugabancin jam'iyyar APC na kasa zai gudanar da taron shugabanni da masu ruwa da tsaki a karo na farko tun bayan ficewar shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki.

Za a gudanar da taron ne ranar Alhamis ta satin da zamu shiga a shelkwatar jam'iyyar ta kasa dake Abuja da misalin karfe 10:00 na safe kamar yadda wani jigo a APC ya sanar da jaridar Premium Times.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnonin APC da shugabannin jam'iyyar na kasa da jihohi zasu halarci taron.

2019: Za a yi wata muhimmiyar ganawa tsakanin Buhari da shugabannin APC na kasa da jihohi

2019: Za a yi wata muhimmiyar ganawa tsakanin Buhari da shugabannin APC na kasa da jihohi

Ana hasashen cewar taron zai tattauna ne a kan zabukan shekarar 2019.

Daga cikin 'yan mambobin kwamitin zartarwa na APC, bayan shugabannin jam'iyyar, akwai shugaban kasa, shugaban majalisar dattijai da kuma takwaransa na majalisar wakilai.

DUBA WANNAN: 2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

Taron gangamin jam'iyya ne kadai ya fi taron kwamitin zartarwa na tara masu ruwa da tsaki a kowacce jam'iyya.

Wannan shine karo na farko da APC zata gudanar da irin wannan taron babu Bukola Saraki da wasu gwamnoni da suka canja sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Gabanin taron na ranar Alhamis, shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin jam'iyyar ranar Talata da yamma.

A yawancin lokuta, shugaba Buhari kan gana da zababbun shugabannin jam'iyyar ne kwana daya kafin taron kwamitin zartarwa, sai dai ana saka ran shugaban kasar zai karbi bakuncin firaministar kasar Ingila, Theresa May.

Ana saka ran jam'iyyar APC zata tattauna batun yadda muhimman bayanai ke zurarewa zuwa ga jama'a tun kafin ta bayar da sanarwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel