Wani dan majalisar dokoki a jihar Cross River ya bakunci lahira

Wani dan majalisar dokoki a jihar Cross River ya bakunci lahira

- Dan majalisa Mr. Simon Nkoro, ya kasance babban mashawarci ga Sanata Liyel Imoke a 2007

- Ya mutu bayan ya yi fama da rashin lafiya

- Gwmanatin jihar Cross River ta aika da sakon ta'aziyyarta bisa rasuwarsa.

Rahotannin da Legit.ng ta samu daga jihar Cross River na cewa, Mr Simon Nkoro, mamba mai wakiltar mazabar Ikom II, a majalisar dokoki ta jihar ya mutu a yau lahadi 26 ga watan Augusta, bayan yayi fama da rashin lafiya.

Mutuwarsa ta zo kasa da wata daya da mutuwar Stephen Ukpekpen, mamba mai wakiltar mazabar Obodu a majalisar dokoki ta jihar, wanda ya yanke jiki ya mutu a watan Mayu, yana tsaka da motsa jiki a garin Ikotenim.

Nkoro wanda yayi dan majalisar dokoki ta jihar har karo biyu karkashin jam’iyar PDP, ya kuma rike mukamin babban mashawarci ga Sanata Liyel Imoke, daga shekara ta 2007 zuwa 2011, gabanin shiga majalisar dokoki ta jihar.

KARANTA WANNAN: Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Da yake bayyana jimaminsa kan wannan mutuwa, Sanata Ben Ayede, gwamnan jihar, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labaran sa Mr. Christian Ita, gwamnan yace: “Mutuwar Hon Nkoro ta girgizamu matuka, sai dai ba zamu iya kalubalantar ubangiji akan hakan ba.”

Ya bayyana Nkoro a matsayin jajurtaccen dan majalisa, dan siyasa mai cike da hikima da dabara, wanda kuma yake aiki kafada-da-kafada da kowa, yana mai cewa mutuwarsa babban rashi ne ga gwamnati da ma al’umar jihar baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel