Ina da yakinin samun tikitin takarar shugabancin kasar nan - Makarfi

Ina da yakinin samun tikitin takarar shugabancin kasar nan - Makarfi

- Zaben 2019 na karatowa yanayin siyasar Najeriya na kara dumama

- Tsohon shugaban PDP ya shaidawa sauran masu neman kujerar takarar shugabancin kasar nan a jam'iyyar cewa su yi hakuri don shi ne zai mata takara

Ahmed Makarfi mai zawarcin tikitin takarar kasar nan a karkashin jam'iyyar PDP ya bayyana cewa yana da yakinin shi ne dan takarar da zai samu damar karbar tikitin takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.

Ina da yakinin samun tikitin takarar shugabancin kasar nan - Makarfi

Ina da yakinin samun tikitin takarar shugabancin kasar nan - Makarfi
Source: Depositphotos

Makarfi ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani da aka yi da manema labarai a jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa, makarfi wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna ne kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na rikon kwarya, shi ma yana daya daga cikin 'ya'yan jam'iyyar ta PDP 12 da suke son shugabantar kasar nan.

‘Dan takarar wanda ya gama wata ganawa da wasu 'ya'yan jam'iyyar dake kudu maso yammacin kasar nan ya ce yana da tabbacin shi ne zai samu tikitin takarar sabida irin nagartar da yake da ita, da kuma irin yadda ya rike jam'iyyar ta PDP wanda hakan zai ba shi dama fiye da kowa.

"PDP ta zama tamkar sabuwar Amarya a yanzu saboda irin cigaban dana kawo mata. Amma kafin zuwa na jam'iyyar ta zama tamkar matacciya".

"Duk cikin 'ya'yan jam'iyyar nan babu wanda yake da irin damar dana ke da ita. Kuma ina tabbatar da cewa zan kawo cigaba da sauyi".

"Tun da na shigo jam'iyyar PDP ban taba ficewa daga ciki ba, gogewar da na samu a matsayin daya daga cikin ‘yan kwamitin kudi na tsawon shekaru takwas zai bani dama wajen samun tikitin takarar kasar nan".

Makarfi ya musanta zargin da ake yi na cewa sai wanda yake da kudi ne yake samun tikitin takara, inda ya bayyana cewa ba lallai ne sai mutum yana da kudi zai samu damar zama shugaban Najeriya ba.

KU KARANTA: 2019: Saraki ya yi kus-kus da wani gwamna a kudancin Najeriya

"Yaushe ne Najeriya ta fara zabar shugaban kasa saboda abun hannunsa? Idan ka duba Alhaji Shehu Shagari, Chif Olusegun Obasanjo, Alh. Umaru Musa Yar'Adua, Dakta Good-luck Jonathan da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari dukkansu sun zama shugabannin kasar nan ba tare da an zabe su saboda kudinsu ba".

"A wata ziyara dana kai kudu maso yammacin kasar nan sun bayyana min cewa akwai dan takar da yake basu kudi da wasu kayayyaki, amma ni ba zan basu ba saboda sun fi kowa sanin na cancanta da wannan gurbi".

Da aka tuntube shi game da bawa mace gurbin mataimakin shugaban kasa, ya ce zai so ace mace ta masa mataimaki in har ya samu damar lashe tikitin takarar.

Ya ce har yanzu mata basu shiryawa karbar kalubalen zama shugaban kasa ko mataimaki ba, wanda hakan ne yasa wannan gurabe suka zama na zama kawai.

"Ina burin ganin wata rana mace ta zama shugaban kasar nan ko kuma mataimakiya, ba wai ko yaushe ake barinsu a baya ba".

Ya zuwa yanzu hukumar shirya zabe ta kasa INEC ta yi wa jam'iyyu har 91 rijista domin fafatwa a zaben 2019.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel