Wani gwamnan APC a Arewa ya kwashi kunyar sa a hannu a wajen taro

Wani gwamnan APC a Arewa ya kwashi kunyar sa a hannu a wajen taro

Labarin ke iske mu na nuni ne da cewa matasa a jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun yi wa Gwamnan jihar ta su Umaru Jibirilla Bindow ihu a wajen taron kaddamar da fara aikin hanyar gwamnatin tarayya a jihar.

Matasan wadanda suka nuna rashin jin dadin su game da salon mulkin gwamnatin jihar sun yi ta yin ihu tare da nuna rashin gamsuwar su a lokacin da ake kirari daga saman mumbarin 'yan siyasar.

Wani gwamnan APC a Arewa ya kwashi kunyar sa a hannu a wajen taro

Wani gwamnan APC a Arewa ya kwashi kunyar sa a hannu a wajen taro
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Abu 5 da Buhari yayi a Daura yayin bikin sallar sa

Legit.ng ta samu cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya yi yunkurin nitsar da matasan inda ya yi kirarin "Najeriya sai Buhari Adamawa sai Bindow". Amma matasan sai suka amsa masa da Najeriya sai Nyako.

Taron kaddamar da hanyan ya samu halartar jiga-jigan siyasar jihar Adamawa ciki har da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta tsohon gwamnan jihar kuma Sanata a majalisar dattijan Najeriya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da matsayin ciwon daji watau kansa.

Haka zalika gwamnan jihar ya bayyana cewa ranar da tsohon uban gidan nasa ya bar jam'iyyar APC ya koma PDP bai yi bacci ba saboda murna don kuwa daman ya zamar masa kadangaren bakin tulu ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel