Zaben 2019: Gwamna El-Rufa'i ya fara juyawa Shugaba Buhari baya

Zaben 2019: Gwamna El-Rufa'i ya fara juyawa Shugaba Buhari baya

Gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin sha-lelen shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari watau Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shi fa ya riga ya nemarwa Sanata Shehu Sani kishiya a zaben gama gari na 2019 don haka ba sulhu.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan Sanata Shehu din dake zaman wakilin jihar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattijai ya kaiwa shugaba Buhari gaisuwar barka da Sallah a gidan sa dake Daura inda kuma ma har Shugaba Buhari din ya karbe shi hannu biyi-biyu.

Zaben 2019: Gwamna El-Rufa'i ya fara juyawa Shugaba Buhari baya

Zaben 2019: Gwamna El-Rufa'i ya fara juyawa Shugaba Buhari baya

KU KARANTA: Labarin dan damfarar da ba a taba irin sa ba a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa sai dai shi Gwamna El-Rufai din a yayin wata zantawa da yake yi da magoya bayan jam'iyyar ta APC a jihar, ya bayyana cewa shi baida matsala da Sanatan amma fa ya riga ya yanke shawarar kin goya masa baya.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta tsohon gwamnan jihar kuma Sanata a majalisar dattijan Najeriya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da matsayin ciwon daji watau kansa.

Haka zalika gwamnan jihar ya bayyana cewa ranar da tsohon uban gidan nasa ya bar jam'iyyar APC ya koma PDP bai yi bacci ba saboda murna don kuwa daman ya zamar masa kadangaren bakin tulu ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel